Robinho ya ce ba zai koma Turkiya ba

Robinho
Image caption Robinho

Dan wasan Manchester City Robinho ya ce bashi da niyar komawa kungiyar Fenerbahce ta kasar Turkiyya a yayinda ya ce yana tattaunawa ne da kungiyoyi a kasar Spaniya da kuma Italiya.

Dan wasan wanda dan asalin kasar Brazil ne yana neman sauyan kungiya kafin a kammala wa'adin sauya 'yan wasa.

Robinho mai shekarun haihuwa 26 ya ce muddin zai ci gaba da taka leda a Turai, yana dai sha'awar komawa Italiya ko kuma Spaniya ne.

Robinho bai takawa City leda ba a kakar wasan bana, tun bayan da ya dawo daga kungiyar Santos daya takawa leda na wucin gadi.