Arsenal ta sayi Squillaci daga Sevilla

Sebastien Squillaci
Image caption Sebastien Squillaci

Arsenal ta kammala sayan dan wasan bayan Faransa dake takawa kungiyar Sevilla leda Sebastien Squillaci.

Rahotanni sunce dan wasan mai shekaru 30 ya sa hanu ne a kwantaragin da sai bugawa Arsenal kwallo na shekaru uku bisa sabanin dokar Wenger na siyan 'yan wasan wadanda shekaru su suka kai 30 na dogon lokaci.

Wenger ya ce: "Muna bukatar dan wasan baya mai kwarewarsa, da kuma daidan kudi, kuma dan wasan ya cimma ma sharudan".

Dan wasan ba zai taka leda ba a wasan da Arsenal za ta buga da Blackburn a karshen mako.

Squillaci zai taimakawa kungiyar bayan barin wasu daga cikin 'yan wasan bayan Arsenal da suka hada da Sol Campbell da William Gallas da kuma Mikael Silvestre.