AC Milan na tattaunawa da Barca akan Ibrahimovic

Zlatan
Image caption Dan kwallon Barca Zlatan Ibrahimovic

Dan kwallon Barcelona Zlatan Ibrahimovic watakila ya koma kungiyar AC Milan ta Italiya, in ji mataimakin shugaban Ac Milan Adriano Galliani.

Akwai alamun Barca da Zlatan din duk sun zaku akan batun sauyin, bayanda dan kwallon ya bar Inter Milan ya koma Nou Camp akan pan miliyan 35 a bara.

Galliani ya ce an fara tattaunawa amma dai dan kwallon na da tsada sosai,kuma zai tattauna da shugaban Barca Sandro Rosell a ranar Alhamis.

Wakilan AC Milan a halin yanzu suna Catalonia bayanda kungiyoyi biyu suka tashi kunen doki wato daya da daya a ranar laraba inda David Villa ya ciwa Barca a yayinda Filippo Inzaghi ya ciwa AC Milan.