Tottenham ta lallasa Young Boys

Tottenham ta tsallake zuwa zagayen rukuni rukuni
Image caption Tottenham ta tsallake zuwa zagayen rukuni rukuni

Kungiyar Tottenham ta doke Young Boys ta kasar Switzerland da ci hudu da nema a wasanni share fage na taka leda a gasar zakarun Turai bugu na biyu.

Peter Crounch ya zura kwallaye uku a wasan a yayinda Jamein Defoe ya zura guda.

A bugun farko da kungiyoyin biyu sukayi a Switzerland, Young Boys ce ta yi nasara akan Tottenham ta da ci uku da biyu.

A sauran wasannin da aka buga kungiyar Auxerre ce ta doke Zenit St. Pete da ci biyu da nema. A yayinda Ajax ta tashi biyu da daya tsakanin ta da Dynamo Kyiv.

Kungiyar KĂžbenhavn ta doke Rosenborg ne da ci daya mai ban haushi, sai kuma Zilina da ta dake Sparta Praha da kwallo guda.