Liverpool da Barcelona sun cimma yarjejeniya a kan Mascherano

Javier Mascherano
Image caption Javier Mascherano sanye da jan riga a lokacin dayake Liverpool.

Liverpool ta yadda da kudin da Barcelona ta ce za ta biya a kan Javier Mascherano, wanda ya nemi ya bar kungiyar tun a watan Yuli.

Shafin kungiyar Liverpool ya ce: "Mun baiwa Barcelona damar tattaunawa da dan wasan".

Liverpool tana so ta mayar da fam miliyan 18 din data sayi dan wasan da shi shekaru uku da rabi da suka wuce daga West Ham.

Ita ma dai kungiyar Barcelona ta bada tabbacin hakan a cikin wata sanarwar : "Kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniya game da sayan dan wasan na tsawon shekaru biyu".

Sanarwar a shafin kungiyar ta Barcelona ta kara da cewa: "Mun cimma yarjejeniyar bayan munyi tattaunawar fahimta tsakanin kungiyar Liverpool da kuma dan wasan".