Obinna Nsofor ya koma West Ham

Obinna Nsofor
Image caption Obinna Nsofor

Dan wasan Najeriya Obinna Nsofor ya koma kungiyar West Ham daga Inter Milan na wucin gadi.

Kungiyar dai ta ce za ta iya siyan dan wasan na dindindin idan ya taka rawar gani a kungiyar.

A kakar wasan bara, dan wasan ya takawa kungiyar Malaga leda na wucin gadi.