Ancelloti ya yabawa 'yan wasansa

Carlo Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya yabawa 'yan wasansa saboda nuna kwarewar da suka yi a wasannin da suka buga a gasar Premier ta bana.

Kocin ya yi yabon ne bayan nasarar da Chelsea ta yi a wasan da ta buga da Stoke City a ranar asabar, inda aka tashi Chelsea tana da biyu Stoke na nema.

Florent Malouda da Didier Drogba ne suka zura kwallayen a wasan.

"Bamu buga yadda muke so ba, amma dai 'yan wasan sun nuna natsuwa da kwarewa." In ji Ancelloti.

"Babu yadda za a yi mu rika zura kwallaye shida kowani mako, abu mai mahimmaci shine mu lashe wasa".

Chelsea ta fara kakar wasan bana ne da wasa tsakaninta da West Brom da kuma Wigan, wanda kuma ta zura musu kwallaye shida kowannensu .