AC Milan ta sayi Ibrahimovic na wucin gadi

Zlatan Ibrahimovic
Image caption Zlatan Ibrahimovic a lokacin da Barcelona ke kece raini da Arsenal

AC Milan ta sayi dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic na wucin gadi daga kungiyar Barcelona.

Milan dai tana da damar sayan dan wasan na dindindin a badi idan ya taka rawar gani a kakar wasan bana.

"Mun sayi dan wasan na wucin gadi a kakar wasan bana, kuma an bamu damar sayan sa na dindindin a karshen kakar wasan, idan har mun amince da taka ledar sa." In ji kungiyar Milan a watan sanarwa data fitar.

Itama dai Barcelona ta amince da hakan: "Mun cimma yarjejeniya da dan wasan da kuma Agent din sa domin ya koma Milan na wucin gadi."