Mourinho ya fusata da canjaras din da Madrid ta buga

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho

Sabon kocin Real Madrid Jose Mourinho ya nuna bacin ransa bayan da kungiyarsa ta buga canjaras da Mallorca.

Duk sabin 'yan wasan da Mourinho ya sayo basu taka rawar gani ba a wasan, amma dan wasan da ya fi kowa tsada da kungiyar ta siya a bara, wato Cristiano Ronaldo shi ya fi nuna kwazo a wasan inda ya kai wasu mugan hare-hare.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci dai Mallorca ta zauna ne a bangaren ta tana kare gida, a yayinda ta ke dan zaburan kai hari, lokaci-lokaci.

Bayan an buga wajen sa'a guda a wasan babu ci Mourinho ya sauya 'yan wasa, inda maye gurbin Canales da Di Maria ya sanya Ozil da Karim Benzema.

Madrid dai ta yi wuta a wasan, amma hakan ta bata cimma ruwa ba a yayinda ta gagara zura kwallo.