Dan kwallon Manchester City Robinho ya koma AC Milan

Robinho
Image caption Dan kwallon Manchester City Robinho

Dan kwallon Manchester City Robinho ya koma AC Milan bayan kulla yarjejeniya ta shekaru hudu.

Dan Brazil din ya tsallake gwajin lafiyarshi a San Siro amma dai ba a bayyana kudin da aka saye shi ba.

Dan shekaru 26 da haihuwa, Robinho ya koma Manchester city a matsayin dan kwallon daya fi kowanne tsada a Ingila a shekara ta 2008 akan pan miliyan 32 da rabi.

Robinho dai a watan Junairun bana ne ya tafi Santos ta Brazil a matsayin aro saboda ya kasa nuna kanshi a kungiyar tun zuwanshi.