Holland ta gayyaci Nistelrooy a karon farko tun 2008

Nistelrooy
Image caption Ruud van Nistelrooy ya ciwa Holland kwallaye sosai

Kocin Holland Bert van Marwijk ya gayyaci Ruud van Nistelrooy don maye gurbin Robin van Persie cikin jerin 'yan kwallon da zasu bugawa kasar leda a wasannin share fage na gasar kwallon kasashen Turai.

Van Persie ya jimu ne a idon sawunshi a wasan da Arsenal ta doke Blackburn Rovers daci biyu da daya a karshen mako.

Tun a shekara ta 2008,rabon da Holland ta gayyaci Nistelrooy wanda keda shekaru talatin da hudu da haihuwa kuma baya cikin tawagar data buga gasar cin kofin duniya a Afrika ta kudu.

Tsohon dan kwallon Real Madrid da Manchester United, Nistelrooy a yanzu yana taka leda ne a Hamburg ta Jamus kuma har ya zira kwallaye uku a kakar wasa ta bana.