Huntelaar ya koma Schalke

Klaas-Jan Huntelaar
Image caption Klaas-Jan Huntelaar

Dan wasan kasar Holland Klaas-Jan Huntelaar ya koma Schalke daga kungiyar AC Milan a kan kudi euro miliyan 14.

Kocin kungiyar Felix Magath ne ya tabattar wa manema labarai hakan inda ya ce: "Mun fuskanci matsala wajen cimma yarjejeniyar siyan dan wasan, amma ina matukar farin cikin da zuwansa kungiyar". Huntelaar, mai shekarun haihuwa 27 ya bar kungiyar Milan bayan shekara guda ne da zuwansa daga Real Madrid. Masana na ganin cewar zuwan Zlatan Ibrahimovic kungiyar ne yasa dan wasan ya sauya kungiya.

A yanzu haka dai ya hade da tsohon abokin wasansa a kungiyar Real Madrid wato Raul a kungiyar ta Schalke.