Seydou Keita zai cigaba a Barcelona har 2014

Keita
Image caption Dan kwallon Mali Seydou Keita

Dan kwallon Mali wanda ke taka leda a Barcelona Seydou Keita ya amince da karin kudi a kwangilarshi don cigaba da kasancewa a Barca har zuwa shekara ta 2014.

Dan shekaru 30 da haihuwa, a baya kwangilar ya kamata ta karke ne a shekara ta 2012 amma a yanzu a duk shekara za a dunga sabunta ta har zuwa 2014 tayin la'akari da yawan wasannin daya buga.

Keita ya kasance dan Mali na farko daya taka leda a Barcelona bayan ya bar Sevilla a watan Mayun 2008 inda ya zama dan kwallo na farko da Pep Guardiola ya saya a matsayin koci.

A shekaru biyun da suka wuce, Keita ya zira kwallaye 12 cikin wasanni 92.