Morientes ya yi marabus daga kwallon kafa

Fernando Morientes
Image caption Fernando Morientes

Tsohon dan wasan Real Madrid da kuma Spain Fernando Morientes ya ce ya yi murabus daga kwallon kafa.

Morientes ya shaidawa manema labarai cewar ya samu damar taka leda a kungiyar Sporting Lisbon amma ya ki amincewa da hakan, saboda yana so ya huta. Morientes wanda ya yi wasa a gaba da Raul Gonzalez a kungiyar Madrid ya taimakawa kungiyar inda ta lashe kofin gasar zakarun Turai guda uku da kuma kofin laliga guda biyu daga shekarar 1997 zuwa 2003.

Dan wasan ya taimakawa kungiyar Monaco a shekarar 2004 a wasan karshe na gasar zakarun Turai, kafin ya koma kungiyar Liverpool a shekarar 2005, inda ya zura kwallaye 12 a wasanni 61 da ya bugawa kungiyar.

Morientes mai shekarun haihuwa 34 ya bugawa kungiyar Valencia kafin ya yi marabus a kungiyar Marseille.