Bayern Munich ta bukaci Holland ta biya diyya akan Robben

Robben da Kyut
Image caption 'Yan kwallon Holland Robben da Kyut

Shugaban kungiyar Bayern Munich Karl Heinz Rummenigge ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Holland ta biyasu diyya saboda lokaci mai tsawo da Arjen Robben ya shafe yana jinya.

Watakila Robben ya shafe sauran watannin bana kafin ya murmure saboda raunin daya samu a cinyarshi a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

A cewar Rummenigge,hukumar kwallon Holland ce keda alhakin raunin da dan kwallon ya samu.

Ya ce"ina tunanin hukumar kwallon Holland ya kamata ta biyamu diyya na tsawon lokacin da baya taka mana leda".