Joseph Yobo ya koma West Ham

Yobo
Image caption Joseph Yobo na daga cikin tawagar Super Eagles a Afrika ta Kudu

Dan kwallon Najeriya wanda ke taka leda a kungiyar Everton ta Ingila Joseph Yobo ya koma West Ham na wucin gadi daga nan zuwa watanni shida masu zuwa.

Yobo ya hade da Obinna Nsofor wanda shi kuma ya bar Inter Milan zuwa West Ham din.

A shekara ta 2002 ne Yobo ya bar Olympique Marseille ya koma Everton.

Rahotanni sun nuna cewar bayan kamalla yarjejeniyar, Yobo zai tafi Najeriya don hadewa da sauran 'yan kwallon Super Eagles a shirye shiryen buga wasan share fage tsakaninsu da Madagascar a karshen mako don neman cancantar buga gasar cin kofin kwallon Afrika.