Moratti na fatan Mourinho zai dawo Inter Milan

Massimo Moratti
Image caption Massimo Moratti

Shugaban kungiyar Inter Milan Massimo Moratti ya ce yana fatan tsohon kocin kungiyar Jose Mourinho zai dawo horon kungiyar nan gaba.

Moratti ya yi wannan furucin ne bayan rahotanni sun ambato Mourinho na cewa yana da sha'awar komawa Italiya aiki nan gaba. Moratti har wa yau ya ce yana da kwarin gwiwa cewar wanda ya maye gurbin Mourinho, wato Rafael Benitez zai kai kungiyar ga gaci. "Inawa Benitez fatan alheri domin inda kwarin gwiwa a kan sa." In ji Moratti.