Kocin Algeriya Rabah Saadane ya yi murabus

Rabah Saadane
Image caption 'Yan kwallon Algeriya maki guda tal suka samu a Afrika ta Kudu

Rabah Saadane ya ajiye mukaminshi a matsayin mai horadda 'yan kwallon Algeriya, kwana guda baya 'yan wasanshi sun buga kunen doki wato daya da daya tsakaninsu da Tanzaniya.

Hukumar kwallon Algeriya ta tabbatar da cewar Saadane ya bada takardar ajiye mukamin ne saboda bai gamsu da sakamakon wasan ba.

Saadane ya fara aikinne shekaru uku da suka wuce,kuma ya jagoranci Algeriya zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a karon farko cikin shekaru 24.

A halin yanzu dai hukumar kwallon Algeria ta ce kocin 'yan kwallon kasar 'yan kasada shekaru 17 Ben Chikha ne zai yi rikon mukamin.