Dan Ingila Micheal Dawson zai yi jinya ta makwanni takwas

Dawson
Image caption Dan kwallon Ingila Micheal Dawson

Dan kwallon Ingila na baya wanda ke taka leda a Tottenham Micheal Dawson zai shafe makwanni shida zuwa takwas yana jinya sakamakon raunin daya samu a wasan Ingila da Bulgaria.

Dawson me shekaru 26 da haihuwa ya turgude gwiwarshi ne da kuma idon sawunshi abinda kuma yasa ba zai taka leda a wasan Ingila da Switzerland na ranar Talata.

Hakan kuma na nufin cewar ba zai buga wasannin gasar zakarun Turai uku da kuma wasanni da dama na gasar Premier.

Ingila bata kira kowa ba don maye gurbinshi.

Abinda hakan ke kara nunawa shibe dan kwallon West Ham Mathew Upson da Phil Jagielka ne zasu buga baya, ko kuma a baiwa Gary Cahill dama ganin cewar ya haskaka a lokacin da maye gurbin Dawson din kafin a tashi wasansu da Bulgaria.