Afrika ta Kudu ta casa Nijer daci biyu da nema

Mphela
Image caption Katlego Mphela ya haskaka a gasar cin kofin duniya

Afrika ta Kudu ta doke Nijer daci biyu da nema a wasan neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika da suka buga ranar Asabar a garin Nelspruit.

Katlego Mphela da Bernard Parker ne suka ciwa Bafana Bafana kwallayenta.

Afrika ta Kudu ta samu damar kara yawan kwallayenta amma sai golan Nijer Kasali Daouda ya hanasu.

Dan kwallon Bafana Steven Pienaar yace"mun samu damar zira kwallaye daya wa amma sai muka barar".

Afrika ta Kudu a nan gaba za ta kara da Sierra Leone da kuma Masar a kokarinta na samun gurbi a gasar da za ayi a Gabon da Equitorial Guinea a shekara ta 2012.