An baiwa kocin Ghana Milovan Rajevac wa'adin kwanaki bakwai

Rajevac
Image caption Milovan Rajevac ya haskaka a Afrika ta Kudu

Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta Ghana GFA ta baiwa kocin Black Stars Milovan Rajevac wa'adin kwanaki bakwai ya sabunta yarjejeniya da ita.

Rajevac me shekaru 56 an bashi damar kulla sabuwar yarjejeniya ta shekaru hudu, amma yaki sanya hannu saboda wani dan bambamci tsakaninshi da Manajanshi.

Shugaban GFA Kwesi Nyantakyi ya ce dole ne Rajevac ya yanke shawara.

Nyantakyi ya shaidawa BBC cewar "idan har bamu sansanta ba, zamu nemi wani".

Rajevac ya jagoranci matasan 'yan kwallon Black Stars zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a Angola sannan kuma suka kai zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya.