Asamoah ya ce yana cikin shiri

Gyan yana takawa Ghana leda
Image caption Gyan yana takawa Ghana leda

Sabon dan wasan Sunderland da Ghana Asamoah Gyan ya ce a shirye yake ya fuskanci kowani irin kalubale a kungiyar ganin irin kudin da kungiyar ta kashe domin sayo shi.

Dan wasan Ghanan ya koma Sunderland ne daga kungiyar Rennes ta Faransa a kan kudi fam miliyan goma sha uku.

Gyan ya taka rawar gani a wasanni da ya bugawa Ghana a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.

"Dama ina da burin komawa Ingila taka leda kuma ina cike da farin ciki da yin hakan." In ji Gyan a hirarsa da BBC.

Dan wasan ya ce ya san kungiyar Sunderland ba kamar Chelsea ba ce da za ta iya siyan dan wasa akan fam miliyan 15.

Gyan ya ce saboda irin kudin da Sunderland ta kashe wajen sayan shi zai tabbatar da cewa kwaliya ta biya kudin sabulu.