Theo Walcott ya samu rauni

Dan wasan Arsenal Theo Walcott ya samu rauni a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin Turai da Ingila ta buga da Switzerland.

Ingila dai ta doke Switzerland ne da ci uku da guda.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 21 ya turgude kafar sahun shi bayan Yves Oehri ya tade shi ana minti goma da fara wasan.

An dai kai dan wasan asibiti nan take inda aka dauki hoton kafarsa ta dama.

Kocin Ingila Fabio Capello ya ce raunin bashi da muni, saboda ya yi magana da dan wasan kuma ya ce zai dawo taka leda nan da makwanni biyu.