Essien ya taimakawa Chelsea ta casa West Ham

Essien da Cole
Image caption Micheal Essien ya ciwa Chelsea kwallaye biyu

Chelsea ta cigaba da haskakawa a kakar wasa ta bana a Ingila bayan ta lallasa West Ham daci uku da daya,nasarar data bar West Ham can kasan tebur.

Dan kwallon Black Stars Micheal Essien ne ya zira kwallaye biyu a yayinda Salomon Kalou ya ci daya abinda ya sanya Chelsea din ta samu maki goma sha biyu daga wasanni hudu da aka buga na gasar premier ta Ingila.

Wannan nasarar ta sa kocin Chelsea Carlo Ancelotti murna inda ya bayyana cewar yanason ya shafe akalla shekaru ashirin a Chelsea a matsayin mai horadda 'yan kwallo.

Sakamakon wasannin na karshe mako:

*Arsenal4-1Bolton *Everton3-3Man Utd *Fulham2-1Wolves *Man City1-1Blackburn *Newcastle0-2Blackpool *West Brom1-1Tottenham *Wigan1-1Sunderland