Algeriya ta nada Abdelhak Benchikha a matsayin koci

Algeria
Image caption Tawagar 'yan kwallon Algeriya

Algeriya ta nada Abdelhak Benchikha a matsayin mai horadda 'yan kwallon kasar don maye gurbin Rabah Saadane wanda yayi murabus a makon daya gabata.

Sanarwar da hukumar dake kula da kwallon Algeriya ta fitar a ranar Litinin ta ce zai fara aiki ne bada jinkiri ba.

Sanarwar ta kara da cewar"nadin zai karawa kocin cikin gida kwarin gwiwa sannan kuma zai kawo daidaito a tawagar kwallonmu".

Saadane ya jagoranci Algeriya zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko cikin shekaru 24, sannan sai ya sanarda yin murabus dinshi a makon daya gabata bayan Algeriya ta tashi kunen doki tsakaninta da Tanzaniya a wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika.