Manchester United za ta sauya Neville a matsayin kaptin

Neville
Image caption Sir Alex Ferguson zai maye gurbin Gary Neville

Sir Alex Ferguson ya bayyana cewar Gary Neville ba zai cigaba da saka kambum kaptin din Manchester United.

Neville shine ya maye gurbin Roy Keane a matsayin skipper bayan ficewar dan kasar Ireland din a shekara ta 2005.

Sai dai a kakar wasanni uku da suka wuce, Neville yayi ta fama da rauni.

Sir Alex Ferguson yace "har yanzu Gary ne kaptin,amma muna duba wani dan wasan da zai dunga bugawa a kowanne mako".

A halin yanzu dai Nemaja Vidic shine yawanci ke saka kambum kaptin, a yayinda ake saran idan Rio Ferdinand ya murmure shine zai cigaba da saka kambum.