Liverpool za ta fuskanci matsala a gasar premier

Reina
Image caption Reina ya ce Liverpool na kasa na dabo

Golan Liverpool Jose Reina ya ce saboda rashin takamammen mai mallakar kungiyar, da kamar yuwa ta shiga cikin kungiyoyi hudu na farko a gasar premier.

Sai dai Reina ya ce kocinsu Roy Hodgson nada damar inganta kungiyar bayan an tashi babu ci tsakaninsu Birmingham.

A watanni biyun da suka wuce,Liverpool ta sauya Rafael Benitez da Hodgson sannan kuma dan wasanta na tsakiya Javier Mascherano ya koma Barcelona ga shi kuma Tom Hicks da George Gillett sun kasa samun wanda zai sayi kungiyar.

Wasa daya dai tal Liverpool ta samu nasara akai a kakar wasa ta bana a yayinda Chelsea wacce ke jan rangama tafi Liverpool din da maki bakwai.