Rafael Nadal ya lashe gasar US open a karon farko

Nadal
Image caption Rafael Nadal na murnar daga kofin US open

Dan Spain Rafael Nadal ya lashe gasar US open na tennis bayan ya doke Noval Djokovic da seti uku da daya a wasan karshe da suka kara a New York.

Wannan nasarar itace babban kofi na tara wato grand slam da Nadal din ya lashe.

Sai dai Nadal din ya ce baya tunanin kamo Roger Federer wanda ya lashe manyan kofuna har guda goma sha shida.

Nadal yace "har yanzu inada nisa tsakanina dashi, saboda haka bana tunanin kamoshi".

Nadal ya hade da Federer da Andre Agassi da Roy Emerson da Rod Laver da Don Budge da Fred Perry da suka lashe gasar French Open da Wimbledon da kuma US Open a shekara guda.