2022:FIFA na rangadi a Qatar

Blatter
Image caption Shugaban FIFA Sepp Blatter

Tawagar jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA sun fara rangadi a kasar Qatar na kwanaki uku don ganin shirye shiryen kasar na daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022.

Tawagar mutane shida ta hada da shugaban hukumar kwallon Chile Harold Mayne Nicholls da Danny Jordan na Afrika ta Kudu.

Kokarin Qatar na daukar bakuncin gasar na fuskantar kalubale da dama, amma dai kasar ta ce za ta shawo kan matsalolin fasaha don magance zafi da kuma kafa cibiyoyin da za a dunga shan barasa don kawar da fargabar mashaya.

Shugaban kwamitin na Qatar 2022 Sheikh Mohammed bin Hamad bin Khalifa Al Thani zasu kirkiro da hanyoyin sanyaya filayen wasa ta yadda 'yan kallo da 'yan kwallo ba zasu fuskanci matsanancin zafi ba.

Qatar ce kasa ta tara da FIFA za ta ziyarta wadanda ke kokarin samun damar daukar gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 ko kuma a 2022.