Tsohon kocin Ghana Rajevac ya koma Al Ahly

Rajevac da Pantsil
Image caption Milovan Rajevac da John Pantsil bayan Ghana ta doke Sudan

Tsohon kocin Ghana Milovan Rajevac ya kulla yarjejeniya da kungiyar Al Ahly ta kasar Saudi Arabiya bayan da yaki amincewa ya cigaba da aiki da Black Stars.

Dan shekaru hamsin da shida,Rajevac ya sanya hannu a kwangilar watanni goma sha takwas da Al Ahly.

A shekaru biyun da suka wuce, Rajevac ya taka rawar gana matuka a Ghana inda ya jagoranci matasan 'yan kwallon kasar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da kuma zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya.

Har wa yau dan kasar Serbiyan ya samu wannan nasarar ne ba tare da jigon dan kwallon Ghana wanda ke taka leda a Chelsea wato Micheal Essien.