Barcelona ce za ta lashe gasar zakarun Turai- Van Gaal

Van Gaal
Image caption Louis van Gaal ya tsorata da Barcelona

Kocin Bayern Munich Louis van Gaal ya ce Barcelona ce tafi kama da kungiyar da zata iya lashe gasar zakarun Turai a bana.

Van Gaal wanda ya jagoranci Bayern a wasan karshe na gasar inda Inter Milan ta samu galaba akansu daci biyu da nema ya bayyana haka ne kafin wasan Bayern da AS Roma na ranar Talata.

Yace"Barcelona ce tafi alamun lashe gasar, sannan idan ba ita ba sai Chelsea".

Bayern za ta hadu da Roma da FC Basel ta Switzerland da kuma kungiyar Cluj ta Romania a rukunin E a gasar zakarun Turai ta bana.

Sai dai a wasanni ukun da aka buga na gasar Bundesliga kawo yanzu,Bayern nada maki hudu ne sannan bata taka leda tare da Arjen Robben da kuma Franck Ribery ba.