FIFA:Har yanzu Masar ce kan gaba a Afrika

blatter
Image caption Shugaban FIFA Sepp Blatter

Kasar Masar har yanzu itace kan gaba a jerin kasashen Afrika a fagen kwallon kafa kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta sanar a ranar Laraba.

Har ila yau Masar ce ta tara a duniya a yayinda Ghana saboda takai zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya ta zama ta biyu a Afrika sannan kuma ta ashirin a duniya.

Afrika ta Kudu wacce ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya itace ta hamsin da takwas a duniya sannan kuma ta goma a Afrika, a yayinda zakarun kwallon duniya Spain ke cigaba da zama ta farko a duniya.

Goman farko a Afrika:

1. Masar (9 a duniya)

2. Ghana (20 a duniya)

3. Ivory Coast (23 a duniya)

4. Gabon (31 a duniya)

5. Nigeria (34 a duniya)

6. Algeria (35 a duniya)

7. Cameroon (37 a duniya)

8. Burkina Faso (39 a duniya)

9. Tunisia (56 a duniya)

10. South Africa (58 a duniya)