Bamu san Portugal na zawarcin Mourinho ba-Real Madrid

Mourinho
Image caption Kocin Real Madrid Jose Mourinho wanda ake cewa 'Special One'

Real Madrid ta ce bata da labarin cewar Portugal na neman Jose Mourinho ya zama mai horadda 'yan kwallonta na wucin gadi saboda wasan neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Turai da Portugal din za ta buga a wata mai zuwa.

Darektan Real Madrid Emilio Butragueno ya ce "na tattauna da sauran manyan jami'an kungiyar kuma sun ce ba suda masaniya akan batun"

Wata jaridar Portugal ta bada rahoton cewar hukumar kwallon kasar na son Mourinho ya zama kocin Portugal a watan Oktoba don ya jagoranci tawagar 'yan kwallon kasar a wasanni biyu.

Portugal ta kori kocinta Carlos Queiroz a farkon wannan watan amma har yanzu bata maye gurbinshi ba.