Roy Hodgson ya jinjinawa 'yan wasan shi

Roy Hodgson
Image caption Roy Hodgson

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya jinjinawa 'yan wasan shi bayan sun taka rawar gani a wasan da suka buga a gasar Europa.

Liverpool dai ta lallasa Steaua Bucharest ne da ci hudu da guda.

Wasan da kuma kocin bai yi amfani da Steven Gerrard da kuma Fernando Torres ba.

Hodgson ya ce duk da cewa bamu yi amfani da kwarrarun 'yan wasan ba, 'yan wasan da suka buga sun taka rawar sosai saboda kwazon su.

Kocin Liverpool din ya ajiye wasu daga cikin 'yan wasan ne saboda wasan da kungiyar za ta buga da Manchester United a karshen mako.