Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sharhin Gasar Premiyar Ingila

Image caption 'Yan wasan Aston Villa

Hausawa dai na cewa, rana ba ta karya..., yau ne muka fara kawo muku sharhi da bayanai kai tsaye, kan gasar cin kofin kwallon kafa na rukunin Premier League, Ingila.

Sharhin wanda a cikinsa za ku rika jin yadda 'yan wasan da ku ka fi sha'awa ke taka leda, sannan kuma masu aiko mana da rahotanni dake yankunan ku, za su kasance tare da ku, don ba ku damar tofa albarkacin bakin ku, a kan yadda kuka ga wasannin.

Za mu kuma rinka tsakuro ra'ayoyin da kuke aiko mana ta wayar salula, da kuma irin muhawarar da kuke tafkawa a dandalinmu na musanyar ra'ayi da muhawara, wato BBC Hausa Facebook.

Mun fara ne da wasan da aka yi tsakanin kulob din Aston Villa da na Bolton inda aka tashi wasa 1-1.

Muna kuma bayar da hakuri ga masu sauraronmu ta akwatin Radiyo da basu samu damr jin shirin gabaki dayansa ba.