Shay Given zai iya tafiya idan yanaso-Mancini

Given
Image caption Kwallo ta wuce Shay Given zuwa raga

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya bayyana cewar golanshi Shay Given na iya barin kungiyar a watan Junairun badi.

Given dai ya daina kamawa City kwallo inda a kakar wasa ta bana Joe Hart ya shiga gabanshi.

Mancini yace:"Na gaya mashi zai iya tsayawa idan yanaso, amma dai ina mutunta ra'ayinshi idan yanason ya tafi, zai iya tafiya".

Mancini ya kara da cewar yasan damuwar da Shay Given ke ciki saboda tunda aka fara kakar wasa ta bana ba a bashi damar kama gola ba.