2018:Beckham ya matsa kaimi don taimakawa Ingila

Beckham da Rooney
Image caption David Beckham da Wayne Rooney suna goyon bayan 'England 2018'

David Beckham zai kaddamarda bukin baje kolin kwallon kafa a Trinidad and Tobago a karshen wannan makon don taimakawa Ingila samun damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 .

Ziyarar ta Beckham tazo daidai da wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasada shekaru 17 wadda mataimakin shugaban FIFA Jack Warner zai halarta.

Beckham dai yayi alkawarin kai ziyara Trinidad a lokacin da ya hadu da Warner lokacin rarraba kasashe zuwa rukuni rukuni a shekara ta 2009.

Warner nada kuri'a guda cikin kuri'u 24 na kwamitin Fifa, kwamitin da zai sanar a watan Disamba masu masaukin bakin gasar cin kofin kwallon duniya a 2018 da 2022.

Shugaban Fifa Sepp Blatter da kuma shugabannin kwamitin Ingila 2018 David Dein da Andy Anson duk suma zasu halarci wasan karshen a ranar Asabar a Port of Spain.

Kwalejin kwallon kafa na David Beckham dai zai horadda matasan 'yan kwallon da kocawa kusan dari biyu.