An damke dan kwallon Sunderland Bramble bisa zargin fyade

Bramble
Image caption An zargin Bramble da fyade a otal

An damke dan kwallon Sunderland Titus Bramble bisa zargin ya yiwa wata mata fyade a wani otal a Newcastle.

An damke dan kwallon ne tare da dan uwanshi Tesfaye Bramble a wani Otal na Vermont a ranar Laraba kuma 'yan sanda nayi mashi tambayoyi.

Dan shekaru ashirin da tara an damkeshi ne bayan 'yan sanda sun kira wayarshi bayan wata mata mai shekaru 20 takai kararshi.

Kungiyar Sunderland kawo yanzu bata ce komai akai ba.

Bramble ya hade da Sunderland ne daga Wigan a kakar wasa ta bana.

Bramble tsohon dan kwallon Ingila na 'yan kasada shekaru 21 a baya ya taka leda a Newcastle United da Ipswich.