Keiran Gibbs na Arsenal ba zai dade yana jinya ba

Keiran Gibbs
Image caption Dan kwallon Arsenal Keiran Gibbs

Dan kwallon baya na Arsenal Kieran Gibbs ba zai dade yana jinya ba sakamakon raunin daya ji a wasansu da Tottenham na gasar kofin Carling.

Kocin Gunners Arsene Wenger yaji tsoron kada ya zamto Gibbs me shekaru 20 ya sake karyewa ne a kafarshi kamar yadda ya faru dashi a bara.

Hoton kafar da aka dauki ya nuna cewar bai karye ba.

Wata sanarwa daga adreshin yanar gizon Arsenal ta ce "keiran ya kuje a kafarshi ta hagu amma muna saran ba zai dade yana jinya ba".