Har yanzu ban sa hannu ba akan kwangila ta da Villa- Houllier

Houllier
Image caption Gerrard Houllier ya daga rigar Aston Villa

Gerard Houllier ya bayyana cewar har yanzu bai sanya hannu ba akan yarjejeniyar shekaru uku a matsayin kocin Aston Villa.

Houllier zai jagoranci kungiyar ne a karon farko a ranar Laraba a wasan kofin Carling tsakaninsu da Blackburn bayan ya bar mukaminshi a hukumar kwallon Faransa.

Tsohon kocin Liverpool din ya hakikance bai sanya hannu ba kawo yanzu akan kwangilar.

Yace"batun baida mahimmanci saboda ina ganin a Liverpool ban sanya hannu ba sai a watan Nuwamba ko Disamba".

Houllier ya amince ya maye gurbin Martin O'Neill a Villa Park kusan makwanni biyu da suka wuce amma yana jiran izini daga wajen hukumar kwallon Faransa inda yake aiki .

Har ila yau ya zauna cikin 'yan kwallo a wasan da Villa ta buga kunen doki tsakaninta da Bolton a ranar Asabar.