Ribery zai yi jinya ta makwanni hudu

Image caption Frank Ribery ya yi jinya ta wattanni biyar a bana

Dan kwallon Faransa Franck Ribery ana saran zai shafe akalla makwanni hudu yana jinyar rauni a idon sawunshi, sannan kuma ba zai buga wasannin gasar zakarun Turai guda biyu tare da Bayern Munich. Dan kwallon tsakiyan ya jimu ne a kafarshi ta dama a lokacin wasan da Bayern Munich ta doke Hoffenheim daci biyu da daya a ranar Talata. Ribery ya shafe watanni biyar yana jinyar gwiwarshi a kakar wasannin data wuce. Kocin Bayern Louis van Gaal yace"Franck ya raunata kuma za a bashi kulawar data dace don ya murmure baki daya". Ganin cewar Arjen Robben watakila ba zai kara taka leda ba a bana, rashin Ribery babbar cikas ce ga Bayern.