'Yan sanda a Faransa sun wanke golan Kamaru Apoula Edel .

Apoula Edel
Image caption Golan Kamaru Apoula Edel

'Yan sanda a Faransa sun wanke golan Kamaru wanda ke taka leda a kungiyar Paris St Germain Apoula Edel cewar baida laifi sam akan batun asalinshi.

Edel ya fuskanci tuhuma ne daga hukumar kwallon Turai UEFA bayan da kungiyar Sevilla ta kai kararshi akan ya boye asalinshi.

Ya tattauna da 'yan sanda a Paris bayan da tsohon kocinsa da ejan din shi Nicolas Philibert suka kai kararshi.

'Yan sanda sun duba asalin Edel kuma sun gano cewar baida matsala.

Philibert wanda yayi kocin Edel a Kamaru, ya baiwa Edel din aron kudi har ya koma kungiyar Almeria , sannan yace dan kwallon nada shekaru 29 bawai 24 kuma sunanshi na asali Ambroise Beyamena.

Edel da PSG sun shigar da takarda akan cewar ana neman bata musu suna.