Kakuta da Benayoun da Kalou sun ji rauni

Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti na cikin damuwa akan raunin 'yan kwallonshi

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce yafi damuwa akan raunin 'yan kwallonshi uku akan kashin da suka sha a hannun Newcastle a gasar kofin Carling.

Yossi Benayoun da Gael Kakuta da kuma Salomon Kalou duk sun sami raunin bayan Chelsea ta sha kashi daci hudu da uku.

Ancelotti yace"ba zasu buga wasanni ba a anan gaba amma dai a ranar Juma'a zamu san tsananin ciwon".

Ya kara da cewar "Kakuta da Benayoun suna da matsala a kafarsu sai kuma Kalou wanda ya raunata cinyarshi".

Sakamakon raunukan da 'yan kwallon suka samu, Chelsea ta buga minti 28 na karshe da 'yan kwallo goma ne.