An nada Hicham el Amrani a matsayin sakataren riko na CAF

Hicham el Amrani
Image caption Sakataren Riko na Caf Hicham el Amrani

An nada dan kasar Morocco Hicham el Amrani a matsayin Sakataren riko na hukumar dake kula da kwallon Afrika wato CAF.

Dan shekaru talatin da daya, El Amrani ya maye gurbin Mustapha Fahmy wanda zai bar Caf ya koma Fifa a matsayin Darektan kula da gasanni.

Amrani zai fara aiki ne daga ranar daya ga watan Oktoba bayan ya fara aiki da Caf a bara.

Shugaban Caf Issa Hayatou ya jinjinawa Fahmy wanda ya shafe shekaru 28 a matsayin babban sakataren Caf.

Fahmy a jawabinshi ido cike da kwalla ya ce wannan matakin nada wuyar gaske a gareshi.