Carling:Hodgson ya nemi afuwar 'yan Liverpool

Hodgson
Image caption Roy Hodgson na fuskantar matsin lamba a Liverpool

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya nemi afuwa saboda fidda kungiyar da Northampton tayi a gasar Carling, inda yace hakan ya kawo musu koma baya.

Liverpool a halin yanzu tana da maki biyar a wasanni biyar na gasar premier ta Ingila kafin wannan kungiyar dake taka leda a rukuni na biyu ta fiddasu.

Hodgson yace"wannan na daga cikin koma bayar da muke fuskanta".

Hodgson ya maye gurbin Rafael Benitez a matsayin kocin Liverpool amma kungiyar har yanzu bata dauki hannu ba a gasar.