Reo-Coker ya ce ba zai bugawa Sierra Leone kwallo ba

Reo Coker
Image caption Iyayen Reo Coker 'yan kasar Sierra Leone ne

Dan kwallon Aston Villa Nigel Reo-Coker ya ki amince da tayin Sierra Leone don ya buga mata kwallo.

Kocin Leone Stars Christian Cole ya bukaci Reo-Coker wanda aka haifa a Ingila ya koma bugawa kasarshi ta gado wato Sierra Leone kwallo.

Dan shekaru 26 da haihuwan ya rubutawa hukumar kwallon Sierra Leone SLFA inda ya bayyana mata cewar yafi son ya bugawa Ingila kwallo.

Reo-Coker yace"na ji dadin gayyatata in bugawa Sierra Leone amma a yanzu zan maida hankali ne a kungiya ta Aston Villa".

Shugaban SLFA Nahim Khadi ya ce baiji dadin wannan matakin da Reo Coker ya dauka ba.