Fernando Alonso ya lashe Singapore grand prix

Alonso
Image caption Alonso direban Ferarri na murnar nasarar da ya samu

Fernando Alonso mai tuka mota kirar Ferari ya lashe tseren Singapore Grand prix bayanda ya shiga gaban Sebastian Vettel na Red Bull tun daga farko tseren har karshe.

Mark Webber na Red Bull ne ya zama na uku duk da cewar yayi karo da Lewis Hamilton direban Mc Laren.

Fernando Alonso bayan ya lashe tseren yace "gasar tayi kurkusa saboda duka mutane biyar din dake kan gaba nada dama lashe gasar, amma dai zamu cigaba da maida hankali don ganin mun samu nasara".

Sai dai har yanzu akan jerin direbobin gasar Formula 1 a yayinda ya rage tsere guda hudu a san gwanin bana, Mark Webber na Red Bull ne kan gaba sai Fernando Alonso na biyu a yayinda Lewis Hamilton da Sebastian Vettel ke na uku dana hudu.