Barcelona ta shiga gaban Real Madrid a Spain

Barca
Image caption Mazajen kungiyar Barcelona

Zakaran gasar Laliga ta Spain wato Barcelona ta shiga gaban abokiyar hamayyarta wato Real Madrid bayan da Barca din ta koma ta biyu a tebur sakamakon nasarar data samu akan Athletic Bilbao da ci uku da daya.

Barca ta samu nasara ce bayan an dawo hutun rabin lokaci inda Seydou Keita da Xavi da Sergi Busquets suka ci mata kwallayen.

Ita kuwa Real Madrid ta barar da damarta ne inda ta tashi babu ci tsakaninta da karamar kungiya wato Levante.

Valencia a yanzu ita ke jan ragamar taburin gasar bayan da ta doke Sporting Gijon daci biyu da nema.

Sakamakon gasar La liga na karshen mako:

*Racing Santander 0 - 1 Getafe *Deportivo La C… 0 - 2 Almería *Espanyol 1 - 0 Osasuna *Mallorca 2 - 0 Real Sociedad

Teburin gasar ya nuna cewar Valencia nada maki 13, sai Barcelona maki 12 a yayinda Real Madrid keda maki 11.