Serie A :Inter Milan na sama a yayinda Lazio ta yinkuro

Inter Milan
Image caption Inter Milan na kokarin kare kofinta duk da tafiyar Jose Mourinho

Inter Milan har yanzu itace kan saman tebur duk da cewar AS Roma ta doke ta daci daya me ban haushi. Lazio a yanzu ta kamo yawan makin Inter amma dai itace ta biyu bayan da Lazio din ta samu galaba akan Chievo daci daya da nema. Brescia kuwa ta sha kashi ne a wajen Bari daci biyu da daya.

Sakamakon gasar Serie A na karshen mako:

*Cesena 1 - 4 Napoli *Bari 2 - 1 Brescia *Chievo 0 - 1 Lazio *Catania 1 - 1 Bologna *Sampdoria 0 - 0 Udinese *Palermo 2 - 2 Lecce *Fiorentina 2 - 0 Parma

Yanzu haka dai Inter Milan ce a gaban da maki 10 sai Lazio ta biyu da maki 10 a yayin Chievo da Brescia keda mako 9.