Bolton Wanderers ta yiwa Manchester United cikas

Owen
Image caption Micheal Owen ne ya farkewa United kwallo na biyu

Manchester United ta barar da damar rage ta zara tsakaninta da Chelsea a gasar premier ta Ingila bayan da ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Bolton .

Zat Knight ne ya fara ciwa Bolton kwallon a yayinda Nani ya farke mata.

Sai kuma Martin Petrov ya na biyu a yayinda Micheal Owen ya farkewa United aka tashi biyu da biyu.

Sakamakon wasan ya nuna cewar da Manchester ta doke Bolton da maki daya ne tsakaninta da Chelsea saboda Manchester City ta doke Chelsea daci daya me ban haushi kamar yadda Arsenal ta sha kashi a gidanta a wajen West Brom daci uku da biyu.

Amma a halin yanzu Chelsea nada maki 15 sai Manchester United maki 12 sai Arsenal maki 11 a yayinda Manchester City keda maki 11.